Yanzu haka maniyyatan jihar Neja ka iya samun sa’ida bayan da ake daf da kammala aikin filin jirgin saman Minna don fara jigilar maniyyatan aikin Hajjin 2024.
Gwamna Umaru Bago, wanda ya bayyana hakan a Minna, ya tabbatar da cewa titin jirgin saman filin jirgin zai rike matsayi na cewa shi ne mafi tsayu kuma mafi inganci a Najeriya.
“Tabbas an kawo karshen jigilar maniyyatan mu daga Abuja,” in ji gwamnan.
“A yanzu filin jirgin yana aiki, ga jirage nan daban-daban, har da na haya gami da na Boeing 747 duk suna sauka a filin jirgin saman. Bugu da kari, filin ya kasance wani mafaka fa ta dace da rundunar an ba shi aiki a matsayin dabarun sa ido ga rundunar sojojin saman Najeriya.
“Shugaban hafsan sojin sama ya ziyarci filin jirgin kuma ya nuna gamsuwa da aikin da aka yi a kan titin jirgin.”
A tuna cewa, bayan duba titin sauka da tashin jiragen sama na Minna, Gwamna Bago bai gamsu da aikin da aka yi ba, sannan ya umurci kamfanin Dantata & Sawoe da su karbe aikin sannan su kammala shi cikin sa’o’i 48, kuma suka yi.
Ya bayyana cewa da yanzu an kammala titin sauka da tashin jiragen sama, hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya, NCAA ta baiwa filin jirgin tabbacin tashi da saukar dukka nau’ukan jirage.