Tinubu ya yi Umrah a Makkah

0
247

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, a jiya Lahadi ya gudanar da ibadar Umrah a Makkah, Saudi Arebiya, inda ya yi addu’ar Allah Ya taimaka masa ya samu nasara a mulkin Nijeriya.

Shugaban ya gudanar da ne bayan kammala taron da ya kai shi ƙasar, a Riyadh babban birnin kasar Saudiyya, inda ya halarci taron Saudiyya da kasashen Afirka.

Babban mataimakin Tinubu na musamman kan harkokin yada labarai, Abdulaziz Abdulaziz ne ya bayyana gudanar da Umrah din da shugaban ya yi a yammacin jiya Lahadi.

A cewarsa, a yayin gudanar da ibadar, shugaban ya yi addu’o’in samun ci gaba a Najeriya tare da neman tsarin Allah domin ya jagoranci kasar.

“Mai girma shugaban kasa Bola Tinubu, bayan kammala taron a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, sai ya zarce domin gudanar da aikin Umrah a safiyar yau a Makkah. Ya yi amfani da wannan damar wajen yi wa Nijeriya addu’a domin daukakar ta da kuma shiriyar Allah a gare shi,” in ji Abdulaziz.