Bisa la’akari da karancin lokacin da ake da shi na shirye-shiryen gudanar da aikin hajji da kuma tsadar aikin hajji,
Kungiyar mai zaman kanta da ke kawo rahotanni kan Hajji da Umrah, wato Independent Hajj Reporters, IHR, ta shawarci hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) da ta rage yawan kamfanonin da ke yi wa alhazai hidima a Saudiyya.
Haka zalika IHR ta shawarci NAHCON da hukumomin alhazai na jihohi da su hanzarta fara kulla yarjejeniya kan kwangiloli na dogon zango da masu gudanar da hidima lokacin aikin hajji na kasar Saudiyya domin rage tsadar farashin hajjin da tashin farashin dala a kan Naira ke haifar wa.
IHR ta ya bayar da wadannan shawarwari a wata sanarwa a yau Laraba mai dauke da sa hannun kodinetan ta na kasa, Ibrahim Mohammed.
“Mu’amala da kamfanonin da ke yiwa alhazai hidima sama da 20 ko fiye a lokacin aikin hajji yana haifar da ƙalubale masu yawa na aiki ga hukumar kula da aikin hajji da kuma hana tsari mai sauƙi,” in ji IHR.
IHR ta kuma ce sauran hidimomi a aikin Hajji ga alhazan Najeriya kamar masauki, ciyarwa da kuma hada-hadar motoci ya kamata su kasance da wasu abubuwa na daidaito.
“Misali, masauki daya ko biyu da masu ba da abinci biyu za su iya yi wa daukacin alhazan Arewa hidima ganin cewa suna da al’adu da gargajiya iri daya, musamman a bangaren abinci.
“Wasu ɗaya ko biyu na iya ba da irin wannan ayyukan ga mahajjatan kudanci ta amfani da sigogi iri ɗaya”.