An zaɓi Alkauthar Travels a kamfanunuwan da za su yi jigilar Hajjin 2024

0
321

An zabi Alkauthar Travels and Tours da ke Abuja a matsayin daya daga cikin kamfanoni masu zaman kansu don yin rijista da jigilar maniyyata zuwa Hajji 2024.

Kamfanin wanda abokin huldar kasuwanci ne ga HAJJ REPORTERS na daya daga cikin kamfanoni 58 da suka samu nasarar tantancewa da hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta yi.

Wasu daga cikin sharuddan da suke sa wa a zaɓi kamfanin jigila sun hada da cika ƙa’idojin gudanar da ayyuka kamar haraji, takardar shedar ƙungiyar sufurin jiragen sama ta ƙasa-da-kasa (IATA), asusun tantancewa, ofishi da ma’aikata da kuma biyan kuɗin ajiya Naira miliyan 25 ga hukumar.

Da take magana da HAJJ REPORTERS a yau Litinin daga Makkah, Saudi Arabiya, inda ta je kammala shirye-shiryen alhazanta, Shugabar Alkauthar Travels, Hajiya Rabi Umar ta bayyana farin cikinta kan cancantar kamfanin nata.

“Ya zo a matsayin babban labari da annashuwa domin a bana, tsarin ya yi tsauri. Hukumar NAHCON ba za ta daga kafa ba a bana kuma ko wanene kai idan ba ka cika sharuddan ba, sai kawai su hana ka. Alhamdulillah, ya zuwa yanzu mun samu nasara,” inji ta.

Hajiya Rabi a ta kuma ce bayan wannan mataki, tana addu’a da fatan hukumar za ta zaɓi kamfaninta a matsayin daya daga cikin goman da za a mikawa mahukuntan Saudiyya bisa sabon tsarin da ma’aikatar Hajji da Umrah ta dauka.