Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya raba kyautar kujerun aikin Hajji ga daukacin wadanda suka yi nasara a gasar karatun Alkur’ani da aka yi a jihar a bangaren maza da mata.
A cewar gwamnan, wadanda suka yi nasara su biyu za su kasance cikin malaman da za su zama jagorori da masu wa’azi ga maniyyatan jihar a lokacin aikin Hajjin 2024.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen kammala karatun kur’ani na shekara wanda aka gudanar a Kaduna, babban birnin jihar a ranar Asabar.
Ya kuma bayar da kyautar kudi ga wadanda suka yi nasara a gasar daga matsayi na daya zuwa na hudu a bangarori daban-daban.
Sani, yayin da yake magana kan aikin Hajji na 2024, ya ce ya kaddamar da wani kwamiti don tabbatar da cewa an gudanar da shirye-shiryen aikin Hajjin 2024 cikin nasara da kuma gyara a kurakuran da a ka yi a aikin na 2023 mai dauke da kalubalen wurin kwana da ciyarwa.
Ya luma lura da cewa mutane da dama sun tuntube shi don neman kwangilar ayyukan Hajji kamar su tufafin aikin Hajji, abinci da wurin kwana da sauransu.
“Abin da nake so na gaya wa duk wanda ya samu kwangilar aikin Hajji, shi ne ya ji tsoron Allah, kuma ya bai wa alhazai abin da ya dace domin su samu addu’ar alhazai, ba fushin Allah ba,” in ji shi.