Gwamna Uba Sani ya naɗa sabon shugaban hukumar alhazai ta Kaduna

0
204

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya nada Malam Salihu Abubakar a matsayin Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan, Muhammad Lawal Shehu.

Sanarwar ta ce an yi nadin ne domin samun nasarar aikin Hajji na 2024.

“Domin tabbatar da nasarar aikin Hajji 2024, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya nada Malam Salihu S. Abubakar a matsayin Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna, tare da dukkan ikon da ke hannun Babban Sakataren Hukumar.

“Sakataren Kwamiti na Musamman kan Aikin Hajji na 2024 zai yi aiki a matsayin Sakataren Gudanarwa na Hukumar. Sauran mambobin kwamitin za su gudanar da ayyukan mambobin hukumar.

“An mayar da Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna, Dokta Yusuf Yakubu Arigasiyyu zuwa Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Kaduna (KEPA) a matsayin Manajan Darakta,” in ji sanarwar.