Ku biya kuɗin ku ga jami’an Hajji kuma ku gujewa ƴan kayi-nayi — Hukumar alhazai ta Kaduna

0
280

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna (KSPWA) ta maniyyatan jihar da su guji yin mu’amala da ƴan kayi-nayi yayin da suke kokarin yin rajistar aikin hajjin badi.

LMaimakon haka, Hukumar ta karfafa yin rajista kai tsaye tare dlga jami’an yin aikin rajista da aka ware a fadin kananan hukumomi 23 da ke jihar.

Shugaban Hukumar, Malam Salihu S. Abubakar, ne ya jaddada hakan a lokacin wani shiri kai tsaye ta rediyo mai suna “Dabarzarku” a gidan rediyon KSMC na Kaduna.

Ya kuma tabbatar wa da mahajjata cewa hukumar ta dauki matakan da suka dace don kare muradunsu da kuma hana duk wani nau’i na cuta da zamba a lokacin biyan kudaden ajiya na Hajji.

Malam Salihu ya ce hukumar ta bullo da wani muhimmin mataki ne ta hanyar samar da takardar shaidar biyan kudi ta musamman da sunan bankin da lambar asusun hukumar domin kaucewa yin mu’amala da kudi da jami’an hukumar.

Ya jaddada cewa an haramtawa jami’an hukumar karbar tsabar kudi daga hannun maniyyata.

“Ayyukan nasu shi ne kawai su yi wa masu biya jagora ta hanyar yin rajista tare da ba su takardun shaidar biyan kudi bayan sun buya,” in ji Malam Salihu.

Shugaban ya kuma kara nanata wa’adin biyan kudin ajiya na aikin Hajji na ranar 31 ga watan Disamba, 2023, ya kuma bukaci maniyyatan jihar Kaduna da su kammala rajistar su don gudun kada a ɓarar da damar.

Ya bayyana kwarin guiwar ganin an gudanar da aikin Hajji cikin kwanciyar hankali a shekara mai zuwa kuma yana fatan cike dukkan kujerun da aka ware wa jihar Kaduna.