Shugaban NCPC ya ziyarci na NAHCON a Abuja

0
182

Shugaban riko na Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Malam Jalal Ahmad Arabi, ya karbi bakuncin takwaransa na aiki, Reverend Dakta Yakubu Pam na Hukumar Masu Kai Ziyarar Bauta ta Kiristoci wato (NCPC).

Pam, ya kawo ziyara NAHCON ne domin mika sakon fatan alheri ga sabon nadadden Shugaban hukumar, Malam Jalal Ahmad Arabi.

A wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a, Fatima Sanda Usara ta fitar ta ziyarar wacce ke lullube da fata nagari, ta yi nuni da fata na gari da burin aiki tare.

Ganin irin kalubalen dake tattare da yanayin Tafiyar kai ziyarorin, Shugaban NAHCON yayi tsokaci kan muhimmancin hadin-gwiwa don cukurkudewar kai-komon dake tattare da tafiya ziyarorin.

Malam Jalal Arabi ya mika godiyarsa ta musamman ga Takwaran aikin nasa na NCPC.

Ya kara haske kan anfanin hakuri da jajircewa wajen musayar kwarewar-aiki tattare da gudanar da tsara jigilar Maniyyata Ziyarar Ibada.

Malam Arabi ya yabawa ziyarar Reverend Pam, inda ya ce abar alfahari ce gare shi.

A nasa bangaren, Babban Sakataren NCPC Rev. Dr. Pam ya bayyana fatan samun nasara na hakika ga Malam Arabi a sabon mukaminsa da kuma a shirye yake don bada cikakken goyon-bayansa.

Ya kara da addu’a ga shugaban NAHCON don cin nasara komin rintsi.

Ya kuma yi nuni da irin sanin da yaiwa Malam Jalal, “to kuwa sai Najeriya da mutane sai sunce Gara-da-Akayi.

Ya kara da cewa sai Ma’aikata da Jama’ar Kasa sunyi bikin nasarori da tarihin da zai Kafa a karshen lamarinsa.