Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da bada rancen Naira biliyan 2.2 biliyan biyu ga hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa domin siyan kujerun Hajji 500 na jihar.
Amincewar ta zo ne a yayin taron Majalisar Zartaswa na Jiha l, wanda Gwamna Umar A Namadi ya jagoranta a ranar Alhamis 28 ga watan Disamba, 2023.
Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Bala Ibrahim Mamsa ne ya gabatar da takardar amincewar bada bashin ga majalisar, inda ya bukaci a mikawa hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa.
A nasa martanin, Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta Jigawa, Alhaji Ahmad Umar Labbo ya nuna godiya ga gwamnan jihar bisa amincewa da bashin domin baiwa hukumar damar samun kujeru kafin wa’adin da hukumar alhazai ta kasa ta kayyade na yin rijistar. alhazai na aikin hajjin 2024 ya cika.