Gwamnan Zamfara ya fitar da N747m domin biyan alhazai kuɗaɗensu

0
420

Hukumar Alhazai ta jihar Zamfara ta fara aikin mayar wa da alhazan jihar su 504 da suka ajiye kuɗaɗe daga 2019 zuwa 2023 kudadensu wanda ya kai Naira miliyan 747.

Shugaban hukumar, Musa Mallaha ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Gusau a ranar Asabar.

Ya ce Gwamna Dauda Lawal ya amince da fitar da Naira miliyan 218 duk wata domin biyan kudaden kashi-kashi daga Disamba zuwa Fabrairu.

Mallaha ya ce hukumar za ta ƙara Naira miliyan 92 a kan kudin da gwamnan ya amince da shi domin mayar da kudaden.

“Gwamnan ya amince da mayar da Naira miliyan 747 ga wadanda suka ajiye kuɗaɗensu, a kashi uku tsakanin Disamba 2023 zuwa Fabrairu 2024.

“Kamar yadda nake magana da ku yanzu, tuni gwamnan ya saki Naira miliyan 218 na watan Disamba a matsayin kashin farko. An rigaya an tura kudin zuwa asusun hukumar,” in ji shi.

“Za mu ba da fifiko ga wadanda suka nuna sha’awarsu ta biyan kudin aikin Hajjin 2024, musamman wadanda suka ajiye wasu kudade ga hukumar,” in ji Mista Mallaha.

Shugaban ya yi alkawarin tabbatar da gaskiya da rikon amana a cikin aikin tare da yabawa gwamnan bisa goyon bayansa ga hukumar.