Hukumar alhazai ta ƙasa ta tsawaita wa’adin rufe karɓar kuɗin aikin Hajji na 2024

0
339

Hukumar Alhazai ta, Ƙasa, NAHCON, ta sanar da tsawaita wa’adin rufe karbar kuɗaɗen aikin Hajjin bana.

A wata sanarwa da mataimakiyar daraktan sashin hulda da jama’a, Fatima Sanda Usara ta fitar a yau Talata, NAHCON, ta ɗage wa’adin zuwa 31 ga watan Janairu.

Ta ce ƙarin wa’adin ya biyo bayan koke-koken da malaman addini da hukumomin jin dadin alhazai na jihohi, gwamnonin Jihohi da sauran masu ruwa da tsaki kan a tsawaita wa’adin.

A cewar Usara, duba da kiraye-kirayen da dumbin al’umma su ka yi kan tsawaita wa’adin ya nuna bukatar samar da dama ga maniyyatan da su ke bukatar zuwa aikin Hajji.

“Don haka NAHCON na da yakinin cewa kafin cikar wa’adin, tare da tallafawa daga takwarorinta, hukumar za ta iya tabbatar da ainihin farashin aikin Hajjin 2024.

“Don haka karin wa’adin ya ba da dama ga sabbin masu rajista don yin hakan kuma a karshen watan Janairu, wadanda ke bukatar cika kudaden su ma za su iya yin hakan.

“Hukumar NAHCON na amfani da wannan dama wajen tunatar da maniyyata da sauran masu ruwa da tsaki cewa ma’aikatar aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta sanya ranar 25 ga watan Fabrairu a matsayin ranar rufe sanya hannu kan duk wasu kwangiloli, wanda ke nuni da kawo karshen biyan kudaden da ake biya a asusun IBAN.

“Da wannan tsawaita wa’adin, ya rage wata guda kenan kafin NAHCON ta kammala biyan dukkan kudaden da suka ajiye a asusunta na IBAN na aikin Hajjin 2024.

“Wannan karin wa’adin, duk da cewa ya wuce jadawalin shirye-shiryen NAHCON, ya nuna yadda Shugaban Hukumar, Malam Jalal Ahmad Arabi ya jajirce wajen ganin an shawo kan matsalolin masu ruwa da tsaki.

“Ya kuma mika godiyarsa ga malaman addini, da hukumomin jiha, da gwamnoni bisa yadda suka bayar da shawarar a madadin mahajjatan.