Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta yi maraba da matakin da Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta dauka na tsawaita wa’adin rufe yin rijistar aikin Hajjin 2024 zuwa ranar 31 ga Janairu, 2024.
Wannan dai ya yi daidai da kiraye-kirayen da malaman addini da masu ruwa da tsaki suka yi na a kara yawan maniyyata aikin hajji.
Shugaban Hukumar, Malam Salihu S. Abubakar ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi ya sanya wa hannu a Kaduna.
Salihu ya yi kira ga dukkan maniyyatan jihar da su yi amfani da wannan damar su kammala biyan kuɗaɗen su na aikin Hajji kafin sabon wa’adin ya cika.
“Karin wa’adin zai ba da lokaci mai mahimmanci ga wadanda ba su yi rajista ba don cika burinsu na yin aikin Hajji,” in ji shi.
Ya tunatar da maniyyatan cewa, za a iya yin rajista ta hannun masu rajista a daukacin kananan hukumomi 23 na jihar.