Ministan Harkokin Waje, Amb. Yusuf Maitama Tuggar, ya tabbatar da yarjejeniyar da aka kulla tsakanin gwamnatin Najeriya da ta Saudiyya na ayyuka a aikin Hajji na 2024.
A cewar wata sanarwa da mai ba wa minista shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabarun sadarwa, Alkasim Abdulkadir ya fitar, an rattaba hannun a jiya Lahadi a Jeddah, Saudi Arabia.
Sanarwar ta kara da cewa, Tuggar, a wata ganawa da ya yi da ministan Hajji da Umrah na Saudiyya Dr Taofiq bin Fawzan AlRabiah, ya kuma tabbatar da cewa aikin Hajji na 2024 zai kasance cikin wani yanayi na sabbin dabaru na tabbatar da an aiwatar da hidimomin Hajji da Umrah a kan lokaci.
Taron tsakanin kasashen biyu ya kuma tabo batutuwan da suka shafi jigilar maniyyata ta jirgin sama, kamfanonin jiragen sama da gwamnatin Najeriya ta amince da su, da wuraren aikin Hajji, da kuma ciyar da maniyyata abinci.
“Mun tattauna hanyoyin inganta ayyukan Hajji da Umra daga bangarorin biyu; wannan tsari ne da a koda yaushe ake bitarsa, kuma daga abin da aka tattauna za a samu ci gaba a aikin Hajjin bana.
“Najeriya ce ta hudu a mafi yawan alhazai zuwa Saudi Arabiya kuma ta 5 mafi girma idan aka zo aikin Umrah,” in ji Mista Tuggar.