Hajjin Bana: Mun kama masaukai masu kyau ga alhazan Kano — Hukumar Alhazai

0
195

A kokarin da ta e yi wajen ganin ta sake inganta jin dadin alhazai bakin Allah, gwamnatin Jahar Kano ta hannun Hukumar kula da jin dadin alhazai ta himmatu wajen samar da masauki mai kyau ga maniyyata aikin Hajin bana

Bisa wannan dalili ne, Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sahalewa Hukumar karakashin jagorancin Darakta Janar, Alhaji Laminu Rabi’u Danbaffa da Shugaban ‘yan hukumar gudanarwarta Alhaji Yusuf Lawan da Daraktan Harkokin aikin Hajji Alhaji Kabiru Muhammad Panda domin su je kasa mai tsarki don tantancewa tare da kama masaukan alhazai

Da yake jawabi, Darakta Janar na hukumar, Alhaji Laminu Rabi’u Danbaffa, ya ce tun lokacin da Hukumar ta mikawa Gwamnan rahoton aikin Hajin 2023, ya umarcesu dasu fara dukkanin wani shirin da ya wajaba don tunkarar aikin Hajin 2024

Laminu ya bawa maniyyata aikin Hajin bana tabbacin cewa shugabancinsa zai yi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin ya inganta walwalarsu fiye yadda ake yi a gwamnatin baya

Yayi amfani da damarsa wajen sake yin kira ga dukkanin wadanda ke da niyyar zuwa aikin Hajin na bana, dasu gaggauta biya kafin wa’adin da Hukumar aikin Haji ta kasa ta sanya ya kare nan da makonni biyu masu zuwa
Hajin 2024 Kano Laminu Rabi’u Danbaffa Masaukin alhazai