Hajjin Bana: Hukumar alhazan Abuja za ta fara bita ranar 3 ga watan Fabrairu

0
187

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Babban Birnin Tarayya (FCT) a Abuja za ta fara gudanar da rukunin farko na bitar alhazai ga maniyyata aikin hajjin bana.

Daraktan hukumar, Malam Abubakar Adamu Evuty wanda ya bayyana hakan a wata hira da yayi da manema labarai a Abuja, ya bayyana cewa ana shirin kaddamar da bitar ne a ranakun Asabar 3 da Lahadi 4 ga watan Fabrairun 2024 a sansanin alhazai na dindindin na FCT dake Basan Jiwa kusa da filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe a Abuja.

A cewar Daraktan, tuni aka hada malaman addinin Islama domin gudanar da shirin da ya ke da nufin shirya maniyyata domin su yi aikin Hajji karbabbe.

Mallam Evuti ya bayyana cewa, za a gudanar da atisayen ne a matakai kamar yadda aka saba domin baiwa alhazai damar samun fadakarwa kan rukunnan aikin hajji da kuma sabbin tsare-tsare da hukumomin Saudiyya da hukumar alhazai ta Najeriya NAHCON suka bullo da su na aikin hajjin bana.

Ya shawarci Alhazan da suka fito daga yankin domin gudanar da aikin hajjin bana da su halarci duk shirye-shiryen da hukumar ta shirya da nufin taimaka musu wajen samun aikin hajji karbabbe.

Ya shawarci mahajjata musamman sabbi da su yi amfani da wannan atisayen da kuma inganta iliminsu na Musulunci kan ayyukan Hajji da shiryarwa ta dace domin samun kimar kudinsu da sauke nauyin da ke kansu na addini.

Don haka Daraktan ya gargadi dukkan maniyyatan da har yanzu ba su dawo da fom din su da suka kammala ba ko kuma su mika fasfo din su ba da su yi hakan don baiwa hukumar damar fara gudanar da takardun tafiya.