YANZU-YANZU: NAHCON ta sanar da kuɗin Hajjin bana

0
268

Hukumar alhazai ta Ƙasa, NAHCON ta sanar da cikakken kuɗin aikin Hajjin 2024.

A baya dai hukumar ta sanar da cewa maniyyata su fara ajiye Naira miliyan 4.5 kafin ta sanar da cikakken kuɗin aikin Hajjin na bana.

Sai dai kuma a wata sanarwa da Fatima Sanda Usara, Mataimakiyar Daraktan Yaɗa Labarai ta NAHCON ta fitar a yau asabar, hukumar ta ƙasa kudin zuwa shiyyoyin ƙasar nan.

A cewar Usara, maniyyata da ga kudancin Nijeriya za su biya Naira miliyan 4,899,000, inda maniyyata daga Arewacin kasar za su biya Naira miliyan N4,699,000 kuɗin aikin Hajjin na bana.

Ta kara da cewa maniyyata da ga Yola ta jihar Adamawa da Maiduguri a jihar Borno da su biya Naira miliyan N4,679,000.

Usara ta bayyana cewa shugaban hukumar, Malam Jalal Arabi ne ya yi ƙoƙarin samo ragin kuɗin aikin Hajjin bayan sasantawa da kanfanunuwan yi wa alhazai hidimomi na kasar Saudiyya.

“Ba dan haka ba, da sai kuɗin aikin Hajjin 2024 ya zama Naira miliyan 6. Yanayin da Kasuwar canjin kuɗaɗe ta shiga a makon da ya gabatd ne ya tilasta sasantawar da kanfanunuwan Saudiyya din,” in ji ta