Tunda an sanar da kuɗin aikin Hajjin bana, saura a bayyana guzurin da za a baiwa alhazai — IHR

0
170

Independent Hajj Reporters, IHR, ƙungiya mai zaman kanta da ke sanya ido da kawo rahotanni kan aikin Hajji da Umrah ta yi kira ga Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, da ta baiyana guzurin da za ta baiwa alhazan bana.

A ranar asabar ne dai NAHCON ta sanar da kuɗin aikin Hajjin bana, inda maniyyata daga kudancin Nijeriya za su biya N4, 899, 000, arewacin ƙasar kuma za su biya N4,699,000, inda maniyyata daga Yola da Maiduguri za su biya N4,676,000.

Sai dai a wata sanarwar da shugaban IHR na ƙasa, Ibrahim Muhammad ya fitar a jiya, ƙungiyar ta yaba wa NAHCON bisa kokarin da ta yi na sansanta wa da Saudi Arabia don rage kuɗaɗen aikin Hajjin na bana.

Amma kuma IHR ta yi kira ga NAHCON da ta baiyana adadin guzurin da za ta baiwa alhazai, kamar yadda aka saba yi.

Ya kuma yi kira ga hukumar da ta guji sanar wa alhazai shirin da ta ke yi na ragin kuɗin aikin Hajji har sai ya tabbata tukunna.