Majalisar Wakilai ta bukaci Tinubu ya saka tallafi a aikin Hajji

0
189

Majalisar wakilai a yau Alhamis ta bukaci gwamnatin tarayya da ta saka tallafin kudin aikin hajjin 2024 domin sauƙaƙa wa maniyyata aikin Hajji zuwa ƙasa mai tsarki.

Majalisar ta kuma umarci kwamitinta mai kula da alhazai musulmai da ya sa hukumar alhazai ta kasa, NAHCON ta yi nazari tare da tantance tsare-tsare da nufin ganin an sauƙaƙa wa maniyyata.

Kiran majalisar ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa Umar Shehu Ajilo ya gabatar a zauren majalisar.

Ajilo, yayin da yake jagorantar muhawara kan lamarin, ya bayyana aikin hajji a matsayin wani muhimmin ginshiki na addinin Musulunci da ya yi umarni da ziyartar masallatai masu tsarki da kuma sauran wuraren tarihi, da dai sauran muhimman ayyukan ibada a kasar Saudiyya.

Sai dai ya bayyana damuwarsa kan yadda farashin hajjin bana ya tsefe har zuwa kusan Naira miliyan 5; adadin da ya ce “bai dace da mahajjata matsakaita da masu karamin karfi ba.”

Ajilo ya ce idan aka yi la’akari da yanayin tattalin arziki da ake ciki, ya zama dole a sake nazari tare da bitar matakai da tsare-tsare da hukumar alhazai ta kasa ta bi wajen isar da kudin jirgi da nufin rage shi, ta yadda za a samu sauki ga maniyyatan.

An amince da kudurin ne baki daya a lokacin da kakakin majalisar Abbas Tajudeen ya nemi jin ra’ayin ƴan majalisar.