Hajjin Bana: Sama da maniyyata 2000 ne su ka rijista a Zamfara

0
156

Sama da maniyyata 2000 ne suka ajiye kudin aikin Hajjinsu a hukumar alhazai ta jihar Zamfara domin gudanar da aikin hajjin bana a kasar Saudiyya.

Kwamishinan dindindin na Da’awa, Hadaya da yada labarai, Alhaji Iliyasu Buhari Maijega ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Gusau a kwanan nan.

A cewarsa, hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta baiwa hukumar alhazai ta jihar Zamfara sama da kujeru 3,000.

Alhaji Iliyasu Buhari Maijega ya ci gaba da cewa, “ya zuwa yanzu muna godiya ga Allah madaukakin sarki kasancewar a halin yanzu mun wuce jahohi da dama a Najeriya wajen gudanar da aikin rajista da biyan kudin aikin Hajjin bana a jihar.

Ya kuma yi kira ga maniyyatan da su yi kokari su cika kuɗaɗen su domin al’amarin aikin Hajji ya ta’allaka ne da kudin canjin waje.

Ya yi fatan gwamnatin tarayya za ta sa baki don saukaka wa maniyyata kar su biya makudan kudade na aikin Hajjin bana na 2024.