Gwamna Ahmadu Fintiri na Jihar Adamawa ya amince da nadin Mustapha Amin, Galadiman Adamawa, a matsayin Amirul Hajji na jihar domin aikin Hajjin 2024.
Babban sakataren yada labaran gwamnan, Humwashi Wonosikou ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Yola a yau Litinin.
Ya ce sauran mambobin sun hada da Farfesa Abdullahi Tukur a matsayin mataimakin shugaban kungiyar, Muhammad Hammanjoda, Sheikh Musa Abdullahi da Ibrahim Abubakar.
Wonosikou, wanda ya ambato gwamnan yana taya tawagar murna, ya bukace su da su tabbatar da amincewar da aka yi musu.
Ya kuma bukace su da su kawo iliminsu da kwarewarsu wajen gudanar da ayyukan Hajji