Hajjin bana: Hukumar Hajji ta South Africa ta shirya bita karo na biyu

0
210

Hukumar Hajji da Umrah ta kasar Afirka ta Kudu ta gudanar da bitar alhazai karo na biyu a jami’ar Oaklands da ke birnin Lansdowne a ranar Lahadin da ta gabata.

Taron ya jawo dumbin maniyyata masu shirin zuwa da kuma al’ummar musulmi, wanda ya zama muhimmin taron bayanai don tabbatar da cewa mahajjata sun shirya tsaf don tafiyarsu.

Taron bitar ya kunshi batutuwa daban-daban da suka hada da Jigilar alhazai daga Afirka ta Kudu zuwa dawowa gida, abubuwan da za a yi tsammani a kasar Saudiyya, da ayyukan da hukumar ke yi a lokacin aikin Hajji.

Likitan alhazai, Dr. Salim Parker ya yi karin haske kan allurar rigakafin da ake bukata domin gudanar da aikin Hajji, da suka hada da cutar zazzabin cizon sauro, ciwon sankarau, da mura.

Ya kuma jaddada mahimmancin rigakafin COVID-19, duk da cewa ba wajibi ba ne, saboda ana iya buƙatar sakamakon a Saudi Arabiya.

A nashi ɓangaren,shugaban hukumar ta SHUC, Ismail Kholvalia, ya yi jawabi ga jama’a kan hidimomin aikin Hajji, inda ya bukaci maniyyata da su hada gwiwa da ma’aikatan hukumar jakadanci na kasar su kuma zama masu nuna halaye na gari a Saudiya.