Ba a yarda a yi Umrah sama da ɗaya a Ramadan na bana ba– Saudiyya

0
325

Ma’aikatar Hajji da Umrah ta ƙasar Saudiyya ta ce bata baiwa alhazai damar yin Umrah sama da ɗaya a cikin watan Ramadan da mu ke ciki ba.

Ƙasar ta shinfida wannan ka’ida ne da nufin rage cunkoson jama’a domin gudanar da ayyukan ibada a cikin watan Ramadan, wanda ke nuna kololuwar lokacin Umrah a shekara.

Ba za a bayar da izinin yin Umrah sau biyu ko fiye da haka ba a cikin wata mai alfarma.

“Wannan matakin an samar da shi ne don saukaka cunkoso da kuma ba da damammaki ga sauran alhazai don gudanar da aikin Umrah cikin walwala da annashuwa a cikin watan mai alfarma,” in ji ma’aikatar cikin wata sanarwa.

A tsarin aikace-aikacen manhajar Nusuk, idan mahajjaci ya nemi izinin yin Umrah sau biyu a cikin watan Ramadan, za a ga wani sako da ke cewa, minNeman izini bai samu ba”. Ma’aikatar ta ba da misali da cewa akwai fa’idodi da dama na yin umrah a cikin watan Ramadan.

Yayin da take jaddada wajibcin samun izini daga neman izinin Nusuk don gudanar da aikin Umrah, ma’aikatar ta jaddada muhimmancin bin su da kayyade lokacin gudanar da ibada.