Hajjin Bana: An buɗe manhajar da maniyyata za su yi rijista daga Australia, Nahiyar Turai da Amurka

0
173

Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta sanar da cewa maniyyata daga kasashen Turai, Australia da nahiyoyi biyu na Amurka za su iya yin rajista a yanzu don aikin Hajjin 2024 ta manhajar Nusuk daga jiya Laraba, 13 ga watan Maris.

Manhajar ta Nusuk na bawa mahajjata daga ƙasashen Turai, Amurka, da Australia damar yin rajista da kama masauki da biyan kuɗin aikin Hajji cikin sauƙi da kuma zaɓar matakin hidimar da su ke buƙata a ɓangaren masauki, abinci, jirgin sama, jagora, da sufuri idan sun sauka a Saudiyya.

Kazalika wannan manhajar na bayar da hidimomi da bayanai da dama ga masu son zuwa aikin hajjin bana domin samun damar gudanar da ayyukan hajji cikin sauki da jin dadi kuma a na samun duk waɗannan ayyukan akan aikace-aikacen Nusuk a cikin harsunan duniya guda bakwai.

Abin lura ne cewa ma’aikatar Hajji da Umrah ta sanar a watan Disambar 2023 cewa za ta ba wa maniyyata ‘yan kasashen waje damar yin rajistar aikin hajji mai zuwa ta manhajar ta Nusuk.

Cibiyar sadarwa ta kasa da kasa (CIC), karkashin ma’aikatar yada labarai ta bayyana cewa mahajjata daga nahiyoyin Asiya, Afirka, Turai, Arewacin Amurka, Kudancin Amurka da Oceania na iya yin rijistar aikin hajji ta manhajar.

Mahajjatan za su iya yin rijistar sunayensu ta hanyar yanar gizo bayan ƙirƙirar asusun kansu tare da ba da adireshin imel sannan su zaɓi ƙasar da suke zaune a halin yanzu daga jerin da aka tanadar.