Ramadan: Saudiyya ta samar da stamfi na musamman a filayen jiragen sama

0
211

Babban Ofishin Fasfo, tare da hadin gwiwar da Ma’aikatar Harkokin Cikin gida da Ma’aikatar Al’adu, sun ƙirƙiro da wani stamfi na musamman da za a rika buga wa a kan fasfo, wanda aka samar da shi domin watan Ramadan na 1445H.

An kirkiro stamfin ne domin murnar zuwan watan mai alfarma da kuma inganta tushen al’adun da aka saba yin su cikin watan Ramadan. Matafiya za su iya samun wannan stamfi na musamman a filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da ke Jeddah da filin jirgin sama na Sarki Fahd da ke Damam a duk tsawon watan Ramadan.

A tare da gabatar da tambarin watan Ramadan, Ma’aikatar Al’adu ta kaddamar da gagarumin aikace-aikace da za ta yi a cikin Ramadan na 1445.

Waɗannan aikace-aikace sun ƙunshi nau’ikan ayyukan al’adu, nishaɗi, da wasanni a duk faɗin Masarautar, waɗanda aka tsara don haɓaka wayar da kan al’adu da godiya ga kyawawan abubuwan zamantakewa da ɗabi’a na Saudi Arabiya.

Har ila yau, yana nuna arzikin al’adu da kasar ke da shi tun tale-tale har ya zo ya tarar da zamani.