Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ƙara kuɗin kujerar aikin Hajji da Naira miliyan 1.9 miliyan, inda yanzu kuɗin suka koma naira miliyan 6.8 kan kujera ɗaya.
Hukumar ta ce hakan ya faru ne sakamakon tashin farashin dala wadda da ita ce ake yin kiyasin dukkanin hidindimun da maniyyata suke bukata.
Mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara ta ce wadanda ba su fara biyan wani abu daga cikin kudin kujerar ba za su biya daga N8,225,464.74 zuwa N8,454,464.74 saboda lokacin da aka fitar da farashin kujerar aikin Hajjin bana dala ba ta yi tashin da ta yi ba yanzu.
Hukumar ta kuma ba maniyyata aikin Hajjin na bana wa’adin zuwa 29 ga watan nan na Maris da ake ciki domin kammala biyan kudin: ” Wadanda suka kasa biya suna da zaɓi biyu ko dai su rubuta a mayar masu da kuɗinsu ko kuma su ajiye kudin har zuwa shekara mai zuwa.”
Hukumar ta ce mutum 49,000 ne suka biya kudin kujerun a farashin baya daga cikin kujeru 75,000 da Saudiya ta ba mahajjan gwamnati yayin da ƴan kasuwa ke da kujera 20,000 wato masu tafiya ta jirgin yawo.
Fatima Sanda ta ce hukumarsu ba ta yi haka ba ne domin hana mutane tafiya aikin Hajjin bana ba: “Burin hukumar alhazai shi ne ta cike dukkan kujerun da aka ba Najeriya 95,000, amman idan yanayi ya zo dole a haka za a ƙarba, mun nemi hukumar Saudiya ta ƙara mana lokaci kuma lokacin yana ƙara ƙurewa, shi ya sa aka ɗauki matakin, idan akwai wanda zai taimaka masu to shikenan, idan babu kuma kowa ne alhaji sai ya biya.”
Hukumar ta ce tun a baya ta nemi tallafin wasu jihohi da masu hannu da shuni saboda ganin an dauke wa Alhazai ko da kudin ciyarwa ne a misha’ir da sauransu saboda abin ya zo wa alhazan da sauƙi.
Ta kara da cewa, “Idan da an samu irin wannan tallafi shikenan idan kuma ba a samu ba to kowa ne alhaji zai cika kusan miliyan biyu kenan”
A baya dai naira miliyan 4.9 ne hukumar ta tsayar waɗanda maniyyata za su biya, inda al’umma ke ta kira ga gwamnatin tarayya da ta bada tallafi domin maniyyatan su samu sauƙi, sai dai hukumar ta ce gwamnatin ta bayar da nata tallafin a wasu fannonin dalilin da ya sa aka samu sauki ma kenan, a cewar jami’ar.