Kungiya mai zaman kanta da ke kawo rahotannin Aikin Hajji da Umrah, Independent Hajj Reporters, IHR, ta bukaci hukumar alhazai ta kasa, NAHCON, da hukumomin jin dadin alhazai na jahohi da su sanar wa maniyyatan Hajjin 2024 ko nawa zasu karba a matsayin kudin guzirinsu.
Kungiyar ta ce ya zama wajibi a ja hankalin hukumar NAHCON da hukumomin alhazai na jihohi cewa kudin aikin hajjin 2024 da suka sanar kawo yanzu bai nuna adadin da za a bai wa maniyyatan a matsayin kudin guziri ba sabanin yadda aka saba yi tsawon shekaru.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kodinetan kungiyar na kasa, Ibrahim Muhammed wanda aka rabawa manema labarai.
IHR ta ce a al’adance NAHCON na sanar da kuɗin aikin Hajji ne tare da baiyana guzurin da za a baiwa maniyyata, in da ta ce ana nufin hakan ne don baiwa mahajjata damar shirya tunaninsu kan nawa za su samu da kuma yin shirinsu na kudi yadda ya kamata.
“Misali, Alhazan 2023 sun biya N2.9m kuɗin Hajji, wanda ya hada da Dalar Amurka 800 kudin guzuri. Ƙididdigar kuɗin aikin Hajji ya ƙunshi abubuwan hidimar gida da na Saudiyya da za a yi wa kowanne mahajjaci.
“Sai dai daga baya hukumar NAHCON da ta gabata ta rage kudin guzurim na 2023 zuwa dala 700 saboda abin da suka bayyana a matsayin bambance-bambancen farashin tikitin jirgi.
“Yanzu dai an sanar da kudin aikin hajjin bana ba tare da bayyana nawa ne kudin guzuri ba duk da an sanar da karin kudin aikin hajji,” in ji IHR.
Kungiyar ta ce ana baiwa mahajjatan kudin guzuri ne a ranar da za su tashi zuwa kasar Saudiyya a matsayin kudaden da ake kashewa a aljihunsu domin baiwa alhazai damar kula da wasu bukatu na kudi yayin da suke kasa mai tsarki.
“Muna kira ga NAHCON da Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohi da su gaggauta sanar da nawa ne guzurin aikin hajjin 2024 ga maniyyata,” in ji IHR.