Yau Jihar Nasarawa za ta rufe karɓar cikon kuɗin aikin Hajjin bana da rijistar maniyyata

0
144

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Nasarawa ta ce za ta rufe biyan karin Naira miliyan 1.918 na aikin Hajjin bana a yau Laraba 3 ga Afrilu, 2024.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta nuna cewa wadanda har yanzu ba su biya cikon su ba sai su yi haka kafin a rufe karɓar a yau Laraba, 3 ga Afrilu, 2024 ko kuma su rasa kujerar aikin Hajjin bana.

Sanarwar ta ce, an tsawaita biyan cikon, wanda ya kamata a rufe tun ranar Alhamis din makon da ya gabata ne saboda sakamakon shigowa cikin ds Gwamnan Jihar Nasarawa da sauran masu ruwa da tsaki su ka yi.

Sanarwar ta ruwaito babban sakataren hukumar, Mallam Idris Almakura ya yi kira ga daukacin ko’odinetocin alhazai na jihar Nasarawa da su gaggauta tuntubar maniyyatan da har yanzu ba su biya cikon ba kafin lokaci ya kure.

Almakura ya yaba da goyon bayan gwamnati da al’ummar jihar Nasarawa bayan karin kudin aikin hajji da NAHCON ta yi ba zato ba tsammani.