A karshe dai, Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON da hukumomin jin dadin Alhazai na Jihohi daban-daban sun fara gudanar da aikin bayar da biza a ranar Juma’a bayan da hukumar ta gudanar da wani taron tattaunawa da jami’an jihohin kasar.
Taron, a cewar wata majiya, ya tattauna hanyoyin da za a bi da kuma sabon tsarin da ma’aikatar aikin Hajji ta Saudiyya ta bullo da shi wajen bada biza da kuma bukatar jihohi su yi takatsantsan da aiwatar da wadannan hanyoyin yayin neman biza.
Fara bayar da biza na nuni da fara wani muhimmin bangaren gudanar da aikin hajjin bana domin babu wani maniyyaci da zai iya shiga kasar Saudiyya ba tare da biza ba.
Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta bude hanyar shiga aikin Hajji a hukumance a ranar 1 ga Maris, 2024.
A ranar 29 ga watan Afrilu ne za a rufe bayar da biza sai dai idan Masarautar ta yanke shawarar tsawaita wa’adin farko wanda aka sanya kwanaki 50 zuwa ranar Arafat.