Maniyyata 135 sun rasa gurbin zuwa aikin Hajjin bana a jihar Plateau

0
160

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Plateau ta ce maniyyata 135 da suka ajiye kudi tun da fari ba za su yi aikin hajjin bana ba.

A tuna cewa Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON a watan Maris ta kara Naira miliyan 1.9 kudin aikin Hajjin 2024 ya zama daga miliyan 4.9 zuwa Naira miliyan 6.8.

Hukumar ta kuma sanya ranar 28 ga watan Maris a matsayin wa’adin da aka ba wa maniyyatan sy kammala biyansu.

Maniyyatan da abin ya shafa daga jihar Plateau a ranar Juma’a su ka garzaya zuwa hukumar alhazai ta jihar domin kammala biyan cikon kuɗin na su, amma ina, ba su samu jami’an da za su karbi kuɗaɗen nasu ba

Jami’in yada labarai na hukumar, Yasir Isma’il, a wata tattaunawa da ya yi da wakilin Daily Trust, ya ce wadanda abin ya shafa ba su iya biyan kudaden ba saboda wa’adin biyan kudin ya cika.

Ya ce tuni NAHCON ta kammala jerin sunayen wadanda za su halarci aikin Hajjin bana, wanda hakan ya sa hukumar ta gaza samun karin kujeru.