Hajjin bana: Katsina ta sanya hannu kan yarjejeniyar kama masauki ga alhazan ta

0
242

Jihar Katsina ta rattaba hannu kan yarjejeniyar kama masauki ga alhazan na Hajjin bana.

A sanarwar da jami’in hulda da jama’a ta hukumar jin dadin alhazai ta jihar, Badaru Bello Karofi ya fitar ta ce Shugaban hukumar, Alhaji Kabir Bature ne ya sanya hannu a madadin Babban Daraktan Hukumar da sauran masu ruwa da tsaki akan aikin Hajji a jihar.

Da ya ke bayani bayan kammala sanya hannu kan yarjejeniyar a Makkah, Saudi Arebiya, Alhaji Bature, mai lakabi Sarkin Alhazai yayi kira ga masu kamfanin da Gwamnatin jihar katsina ta amince da shi ya bada masaukan da suji tsoron Allah tare da tabbatar da ingancin ayyukan su.

Ya tabbatar da cewa, Gwamnan Jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Radda a tsaye ya ke wajen ganin maniyyatan Hajjin bana daga Jihar sun gudanar da aikin Hajjin su cikin koshin lafiya.

A nashi jawabin, Shugaban kamfanin, Alhaji Abdulkadir, wanda dan asalilin Jihar Katsina ne da ke zaune a birnin Makkah ya tabbatar da cewa masaukan da za su ba maniyyatan Jihar masu inganci ne.

Ya kuma yi godiya ga gwamnatin jihar akan dama da ta basu tare da alwashin sauke dukkan hakkokin maniyyatan dake kansu kamar yarda akayi yarjejeniyar.