Majalisar Dokokin Kebbi ta yaba da shirin aikin Hajjin bana a jihar

0
194

Kwamitin Kula da Harkokin Addini a Zauren Majalisar Dokokin Jahar Kebbi ya yaba da tsare-tsaren Hukumar Jin Daɗin Alhazzan Jahar a yayin ziyarar da kwamitin yakai a jiya talata.

Shugaban Kwamitin Kula da Harkokin Addini a Zauren Majalisar Dokokin Jahar Kebbi, Hon Tukur Shanga tare da Mambobinsa da suka hada da Hon. Garba Bena, Hon. B.B Birnin Yauri, Hon. Faruku Jega, Hon. Abubakar Besse da Hon. Yusuf Tilli sun kai ziyarar aiki a Hukumar Jin Daɗin Alhazzai ta Jahar Kebbi domin ganin irin tsare-tsaren da Hukumar za ta yi amfani da shi a yayin aikin Hajjin bana.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Ibrahim Sidi Muhammad Jefa ya fitar, ƴan majalisar sun yaba da ƙoƙarin da Shugaban Hukuma, Alh Faruku Aliyu Enabo ya yi da kuma Gwamnan Kebbi, Dr. Nasir Idris Ƙauran Gwandu kan sabunta wurin, wanda hakan yasa yan Kwamitin suka tabbatar da gamsuwarsu akan abinda suka gani.

“Hon. Tukur Mohammed Shanga ya bayyana cewa cike suke da mamaki, ganin har abinda basu sanya ba na gyara sun ga Hukumar ta zo dashi. Hon. Shanga ya nuna jin daɗinshi tare da yabawa Mai girma Gwamna kan jawo wannan jajirtaccen Shugaba ya ɗorashi a wannan Hukumar.

“Shugaban Hukumar, Alh Faruku Aliyu (Jagaban Gwandu) yayi godiya ga Kwamitin bisa ga gamsuwar da sukayi da yadda Hukumar ta tsara ayukkan ta, ya ƙara da cewa duk abinda aka gani na cigaba ƙoƙarin Mai girma Gwamnan Kebbi ne, saboda sai da amincewar shi ne za’a iya canza muhalli da kuma tsarin Hukumar.

“A karshe jagaban gwandu yayi godiya ga Allah tare da kara godiya ga maigirma Gwamna Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu da kuma karin godiya ga yan kwamitin kula da addini a zauren majalisa bisa ga wannan ziyara,” in ji sanarwar