Hajjin bana: Hukumar Alhazai ta ƙaddamar da rabon tufafin mahajjata a Jihar Kebbi

0
188

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jahar Kebbi ta ƙaddamar da rabon tufafin alhazai da jakankuna manya da kanana.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jahar Kebbi, Hon Abubakar Bambu Bagudo ne ya ƙaddamar da rabon kayan da suka hada da yadi ga Maza, Atamfa guda 2 ga Mata, da Hijabi da jikkuna manya da kanana.

A sanarwar da makamin hukumar, Ibrahim Sidi Muhammad Jega ya aike wa HAJJ REPORTERS, Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai na Jahar Kebbi, Alh. Faruku Aliyu ya bayyana cewa wannan gudunmuwa ce da Gwamnan jihar, Dr. Nasir Idris da matanshi, Hajiya Zainab Nasir Idris da Hajiya Nafisa Nasir Idris suka baiwa maniyyatan jihar.

Majalisar dokokin jihar ta yaba da ƙoƙarin gwamnan akan ƙara inganta aiyukan hukumar da kuma zakulo hazikin matashi Alh. Faruku Aliyu a matsayin shugaban ta, wanda acewar ta an dora kwarya a gurbinta.

Kaza-lika, an gabatar da addu’a ga Gwamnan jahar Kebbi da Najeriya ba ki daya.