YANZU-YANZU: Ladanin Masallacin Haramin Makkah na halin tsananin rashin lafiya

0
179

An garzaya da Ladanin Masallacin Harami na Makkah, Ahmad Basnawi zuwa asibiti sakamakon tsananin rashin lafiya.

Shafin Haramain na kafar X ya rawaito cewa ya zu haka Basnawi na ɗakin kula da rashin lafiya mai tsanani.

Shafin ya yi addu’ar Allah Ya bashi lafiya domin ya dawo ya ci gaba da yin aikin Allah, Ya kuma baiwa iyalin sa hakuri da juriya a wannan hali da su ka tsinci kan su, Ameen.

Mu ma daga nan Hajj Reporters mu na masa addu’ar Allah Ya bashi lafiya.