Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kwara ta ce sama da mahajjata 100 daga jihar ba za su halarci aikin Hajjin bana ba.
Sakataren zartarwa na hukumar, Alhaji AbdulSalam Abdulkadir ne ya bayyana hakan a ranar Lahadin da ta gabata yayin wani shirin wayar da kan alhazai da aka gudanar ga maniyyatan jihar.
Ya ce wadanda abin ya shafa su ne wadanda ba za su iya biyan cikon karin Naira miliyan 1.9 da aka kara akan kudin aikin Hajjin bana ba.
Hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON, ce ta kara Naira miliyan 1.9 kudin aikin Hajjin bana, inda ta ce wadanda suka ajiye Naira miliyan 4.9 a yanzu za su cika Naira miliyan 1.9, ya zama miliyan 6.8 kenan gaba daya.
Abdulkadir ya ce, “Kashi 95 cikin 100 na maniyyatan da za su yi aikin hajjin bana sabbin zuwa ne. Sai dai muna da maniyyata sama da 100 da ba za su iya biyan cikon Naira miliyan 1.9 ba.”
Ameerul Hajji na jihar, Sanata Ibrahim Yahaya Oloriegbe, yayin da ya bukaci yin hakuri, ya tabbatar wa alhazan cewa za su tashi daga jihar zuwa Saudia a wannan karon.