Hajjin bana: An kammala bitar alhazai a Katsina

0
125

An Kammala bitar Alhazai a Shiyyoyin Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Katsina guda bakwai.

Da ya ke jawabi ga maniyyatan daga shiyyar Katsina a wajen rufe bitar, Shugaban ma’aikatan hukumar, Alhaji Kabir Bature Syayi kira gare su da su ci gaba da kara neman ilimin yanda za su gudanar da aikin Hajjin nasu domin su sami Hajj mabrur.

Ya kuma yi bayani akan tsare tsare da shirye shiryen da Gwamnatin Jihar Katsina take gudanar wa domin tabbatar da kowane maniyyaci daga Jihar yayi Aikin Hajjin shi cikin kwanciyar hankali.

Alhaji Kabir ya kara jaddada wa maniyyatan cewa Gwamnatin Jihar, karkashin Jagorancin Gwamna Dikko Umar Radda, da hadin gwiwa da hukumar alhazai sun sama wa maniyyatan masaukai a birnin Makkah masu kyau tare da masu dafa musu abinci da zai kasance mai inganci.

A Nashi Jawabin Daraktan tsare tsare na Hukumar, Alhaji Yusuf Ahmed ya shaida wa maniyyatan tsare-tsaren da hukumar keyi tare da sauran takwarorinta na kasa da kuma Kasa Mai tsaki akan Aikin Hajji na bana.