Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta ce ta saka sama da Naira biliyan 18 a asusun Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, domin gudanar da shirye-shiryen aikin hajjin 2024 mai zuwa.
Darakta Janar na hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ne ya bayyana haka a wata ganawa da jami’an ofishin NAHCON na Kano a ofishin sa a jiya Talata.
Danbappa ya bayyana cewa yayin da maniyyata 3,110 suka nemi izinin zuwa aikin hajji, da yawa daga cikinsu kuma suna jiran biza daga NAHCON.
Ya bukaci hukumar da ta gaggauta gudanar da aikin bizar kafin cikar wa’adin rufewa.
Danbappa ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na kammala gyare-gyaren da ake yi a sansanin Hajji kafin a fara jigilar aikin Hajji.
Ya ce ba kamar shekarar da ta gabata ba, gwamnati ta tabbatar da samar da dukkan kayan aikin da ake bukata a sansanin alhazai domin saukaka wa alhazai.
A nata jawabin, shugabar gudanarwa a ofishin hukumar alhazai ta jihar Kano, Hajiya Rabi D’nyako, ta bada tabbacin hukumar ta himmatu wajen magance matsalolin da suka shafi biza.