HAJJIN BANA: Tawogar farko ta Jami’an NAHCON za su tashi zuwa Saudiyya gobe

0
174

Tawogar farko ta mutum 43 ta jami’an Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, za su tashi zuwa Saudi Arebiya a gobe Lahadi domin karasa shirye-shiryen tarbar alhazan Nijeriya.

Tawogar, ɗauke da ma’aikatan NAHCON 35 da kuma likitoci 8 za su tafi su tarbi alhazan Nijeriya na farko wadanda za su taso daga jihar Kebbi a ranar Laraba, 15 ha watan Mayu.

Da ya ke jawabin bankwana a shelkwatar NAHCON, shugaban hukumar, Malam Jalal Arabi ya taya su murna.

Malam Arabi ya kuma hore su da su yi aiki tukuru kuma tsakani da Allah don ganin an samu nasarar aikin Hajji na bana.