HAJJ 2024: NAHCON ta yaba wa gwamna Radda bisa biya wa alhazan Katsina kuɗin Hadaya

0
190

Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, ta yaba wa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda bisa biya wa ɗaukacin alhazan jihar kuɗin hadaya, wani rukuni na aikin Hajji.

A wata sanarwa da kakakin hukumar jin dadin alhazai ta jihar Katsina, Badaru Bello Karofi ya aike wa HAJJ REPORTERS, NAHCON ta yi wannan yabo ne lokacin da Kwamishinan ta da ke kula da Shiyyar Arewa-maso-Yamma, Sheikh Muhammad bin Usman ya kai ziyara hukumar.

Ya ce Bin Usman ya kuma jinjina wa gwamnan bisa alkawarin da ga dauka na baiwa alhazan barks da Sallah a can kasa mai tsarki.

Ya kara da cewa Bin Usman, a yayin ziyarar, ya kuma yaba da gamsuwa da shirye-shiryen hukumar alhazzai ta jihar na fara jigilar alhazan bana nan bada dadewa ba.

Da yake maraba da Kwamishinan , Ciyaman na kwamitin gudanarwa na hukumar, Alhaji Kabir Bature Sarkin Alhazai a Madadin Babban Darakta da sauran masu ruwa da tsaki akan Aikin Hajji, ya shaida wa Kwamishinan cewa Gwamnatin Jihar tayi tsare-tsare da yawa akan aikin Hajjin bana domin maniyyata su yi ibada cikin sauki.

Bature yace cikin shirye-shiryen da hukumar tayi sun hada da daukan nauyin biya wa maniyyatan kudin hadayar su tare da alƙawarin basu goron Sallah.

“Ya kuma tabbatar wa da Kwamishinan cewa Gwamnatin Jihar Katsina tare da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Katsina sun kusan kammala Dukkan Shirye Shiryen karshe na fara Jigilar Alhazan Jihar Katsina,” in ji sanarwar.