Hajji 2024: Kwamishinan NAHCON ya ziyarci Hukumar Alhzai ta Jihar Katsina

0
253

A yayin da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ke ci gaba da shirye-shiryen ƙarshe na fara jigilar maniyyatan Hajjin bana, Kwamishina mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma a Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa, Muhammed bin Usman, ya Ziyarci Hedikwatar Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Katsina.

Waɗanda suka tarbe shi yayin ziyarar sun haɗa da Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Hukumar, Alhaji Kabir Bature Sarkin Alhazai da Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama da wasu daga cikin mambobin hukumar gudanarwa haɗa da wa Daraktocin Hukumar.

Kwamishina Muhammed ya ce, ya ziyarci Hukumar Alhazai ta Jihar Katsina ne domin cika wasu daga cikin dalilan da suka kai shi jihar.

Yayin ziyarar, jami’in ya zagaya domin duba wasu daga cikin wuraren da aka shirya na karɓar maniyyatan bana daga jihar domin tafiyar su ƙasa maitsarki, inda ya yaba da abin da ya gani.

Daga bisani, ya yaba da ƙoƙarin da Hukumar ta yi na tsare-tsaren fara jigilar maniyyatan jihar wanda za a fara kwanan nan.

Haka Kuma, Kwamishinan ya jinjina wa Maigirma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, PhD, a kan tallafin ɗauke wa dukkan maniyyatan da suka fito daga Jihar Katsina yin Hadaya har da ƙarin alƙawarin bai wa ɗaukacin maniyyatan ‘Goron Sallah’ idan Allah Ya kai mu lokaci a Ƙasa Maitsarki.

Tun farko, sa’ilin da yake jawabin maraba ga baƙon, Shugaban Hukumar, Alhaji Kabir Bature Sarkin Alhazai, a madadin Babban Daraktan da sauran masu ruwa da tsaki a kan aikin Hajjin, ya shaida wa Kwamishinan cewa Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Dikko Umar Radda, ta yi tsare-tsare da yawa a kan aikin Hajjin wannan shekarar don tabbatar da kowane maniyyaci ya ya sauke farali cikin kwanciyar hankali.

Kabir Bature ya ƙara da cewa, cikin shirye-shiryen da Hukumar ta yi sun haɗa da ɗaukar nauyin biya wa maniyyatan kuɗin Hadayarsu tare da alƙawalin ba su goron Sallah.

Ya kuma tabbatar wa da Kwamishinan cewa Gwamnatin Jihar Katsina tare da Hukumar Alhazai ta Jihar Katsina sun kusa kammala dukkan shirye-shiryen ƙarshe na fara jigilar Alhazan Jihar Katsina.

PRO PWBKT Badaru Bello Karofi