Hajjin bana: Amirul Hajji na Katsina ya gana da mahukunta hukumar hajji ta jiha

0
132

Amirul Hajj kuma tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Tukur Ahmed Jikamshi ya gana da mahukuntan Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar.

Taron, wanda ya gudana a shelkwatar hukumar, shine karo na farko da Amirul Hajjin ya gana da mahukuntan.

Da ya ke jawabi, Amirul Hajjin ya ce dalilin taron shine domin ya tattauna da mahukuntan hukumar domin su ji tsare-tsare da shirye-shiryen Shiryen da hukumar tayi tunda ga farkon fara shirin aikin Hajjin bana.

Amirul Hajjin yayi kira ga masu ruwa da tsaki na hukumar dasu ba tawagarsa goyon gaya da hadin kai domin samun nasarar aikin Hajjin bana.

Ya kuma tabbatar musu da cewa shi da sauran membobin kwamitin za su ba dukkan masu ruwa da tsaki akan aikin Hajjin na bana domin tabbatar da kowane maniyyaci ya gudanar da aikin Nashi cikin jin dadi.

Daga karshe an zagaya da Amirul Hajjin tare da sauran membobin shi da kuma wasu daga cikin ƴan kwamitin gudanarwa na hukumar.