Hukumar Alhazan Najeriya, Nahcon na ci gaba da jigilar maniyyatan ƙasar zuwa ƙasa mai tsarki domin sauke farali.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce zuwa yau Asabar da safe jirage 12 ne ɗauke da maniyyatan ƙasar 5074 suka isa Saudiyya.
Hukumar ta ce 11 daga cikin jiragen sun sauka ne a birnin Madina, yayin da ɗaya kuma ya sauka a Jedda.
Nahcon ta ce daga cikin adadin maniyyatan da suka isa ƙasa mai tsarkin 2934 maza ne, yayin da 2140 kuma mata ne.
A makon nan ne dai hukumar Alhazqan ta fara jigilar maniyyatan ƙasar, inda aka fara da jihohin Kebbi da Bauchi da Nasarawa da Legos da kuma birnin tarayya Abuja.
BBC Hausa