Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudi Arebiya ta kirkiro da wata hula mai lema domin amfanin alhazai su kare kan su daga zafin rana.
Lemar irin ta ce ta farko kuma za a iya yin Sallah da ita ba tare da takura ba kuma har a yi sun hada yayin da ta ke kan alhaji.
A jikin lemar, akwai aljihu da zai baiwa alhazai damar ajiye kayayyaki kamar su ruwa da dardumai sallah.
An kera lemar kuma domin ta kare alhaji daga zafin rana tun daga hidimar ta har faduwar ta.