Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ta koka kan yadda alhazan Najeriya ke ci gaba da safarar kola zuwa kasar Saudiyya.
Shugaban tawagar masu karbar baki na NAHCON a Madina, Labaran Abdullahi, ya ce matakin na kawo kalubale ga ayyukanta domin yana kawo tsaiko a tashoshin jiragen sama.
Abdullahi ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai a birnin Madina mai alfarma a jiya Lahadi, inda ya bayyana cewa hukumar ta bullo da sabbin tsare-tsare don tabbatar da cewa maniyyata sun isa masaukansu cikin gaggawa daga filayen jiragen sama.
“Gwamnatin Saudiyya na hana mutane zuwa da goro. Wadannan su ne manyan batutuwa. A kodayaushe muna gaya wa ko’odinetocin alhazai na jaha da su hana alhazai zuwa da goro domin hakan ne ke kawo mana tsaiko amma muna aiki da su cikin kwanciyar hankali. An samu hadin kai tsakaninmu da alhazai,” inji shi.
Ya kara da cewa wata matsalar da hukumar ke fuskanta ita ce ta yadda maniyyata suke ajiye fasfo dinsu a cikin jakunkuna bayan an kammala tantance su a Najeriya.
“Wasu daga cikin su za su sanya fasfo dinsu a cikin jakunkunansu cikin kuskure, don haka zai yi wuya su dauko su idan sun isa Saudiyya saboda an dauke jakankunan zuwa guraren daukar kaya ,” inji shi.
Sai dai ya ce hukumar na samun nasara saboda hadin gwiwar gwamnatin Saudiyya.