Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, ta ce saboda ƙarancin kuɗaɗe ta dakatar da wasu alawus-alawus na ma’aikatanta a yayin gudanar da aikin hajjin bana.
Shugaban Hukumar NAHCON, Malam Jalal Arabi, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktar hulda da jama’a ta hukumar, Fatima Sanda-Usara, ta fitar a yau Alhamis a Abuja.
Arabi ya bayyana cewa matsalar kudade da ta shafi bangarori da dama na ayyukan hajjin 2024 ba ta bar alawus-alawus din ma’aikatan NAHCON ba ma a hajjin ba.
Ya ce hukumar ta yi nadamar kasancewar yanayin duba da yadda ma’aikatan ta ke aiki tukuru a yayin aikin Hajji.
“Saboda wadannan matsalolin kudi, wasu alawus-alawus na musamman ga ma’aikatan NAHCON za su ci gaba da kasancewa a dakatar da su har zuwa yanzu.