Daraktan ayyuka na hukumar Alhaji Muhammad Garba ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan rediyon Najeriya a Dutse babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa hukumar ta sake sanya tsarin hada kai domin tabbatar da jin dadin alhazai.
Daraktan ayyuka ya ci gaba da bayyana cewa, an fara hada tsarin ne bayan kowane mahajjaci ya biya kudin aikin Hajji, inda aka fara aiki da biza ta hanyar loda bayanan duk wani mahajjaci.
Ya kara da cewa a halin yanzu hukumar tana da rukuni 31 da suka kunshi mahajjata 45 kowannensu domin tabbatar da cewa kowane rukuni yana da jami’in da zai jagorance shi a duk lokacin da za a gudanar da aikin hajji a Makka da Madina.
Ya ce hukumar ta nada jami’in ga kowane rukuni da zai sa san kowa a duk tsawon wannan aikin hajji.
Muhammad Garba ya ce a yanayin da mahajjatan karamar hukuma ba su kai 45 ba, za a hada su da wata karamar hukuma domin a kara.
Ya ci gaba da cewa rukuni zai taimaka wajen zakulo mahajjatan da ke da alaka da rashin lafiya kamar ciwon sukari da sauransu.
Ya yi nuni da cewa, za a yi la’akari da wadancan alhazan ta fuskar ciyarwa, musamman a Makka.
Ya ce hukumar jin dadin alhazai da ke kula da masaukin alhazai a garin Makka, ta yi ta shirye-shiryen yadda za ta ware dakuna ga duk wani mahajjaci daga Najeriya.
Ya kuma yi nuni da cewa za a raba masaukin ne bisa la’akari da karamar hukumar kowane mahajjaci.
Alhaji Muhammad Garba ya kara da cewa wannan manufa za ta taimaka wa hukumar wajen ganin kowane mahajjaci ya samu nasarar gudanar da aikin hajji cikin nasara.
Ya bukaci daukacin jami’ai da kuma mahajjata da su ba hukumar hadin kai domin cimma burin da ake so.
source: Radio Nigeria