Hukumomi a Masarautar Saudiyya sun bayyana cewa, maniyyata ƴan kasashen waje miliyan ɗaya ne suka isa Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin 2024.
Rahoton da Saudi Gazette ta fitar ya bayyana cewa, ya zuwa karshen ranar Lahadin da ta gabata, adadin maniyyata 935,966 ne suka isa ta jirgin sama, tashoshin jiragen ruwa da mota.
A tuna cewa sama da maniyyata miliyan biyu ne ke halartar aikin hajjin a duk shekara a Makkah inda ake sa ran ƴan Najeriya dubu 65,000 za su yi aikin na bana.
Tuni dai hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta ce ta kwaso alhazan Najeriya 40,696 a jimillar jirage 96.
Rahoton ya ruwaito babban daraktan kula da fasfot (Jawazat) na cewa mafi yawan mahajjata sun zo ta jirgin sama kuma adadinsu ya kai dubu 896,287, yayin da adadin da suka isa ta hanyoyin shiga ta kasa ya kai 37,280 mahajjata, kuma alhazai 2,399 sun zo ta tashar jiragen ruwa.