HAJJ 2024: Jirgin farko na alhazan Katsina 556 ya sauka a Madina

0
210

Jirgin farko na Maniyyatan Aikin Hajjin Bana na Jihar katsina ya sauka lafiya da sanyin safiyar yau Alhamis a Birnin Madina.

Maniyyatan, su kimanin 556 sun bar filin sauka da tashi jiragen sama na King Abdullazeez da ke Jiddah Zuwa Birnin Madina da misalin ƙarfe 12 na dare, sun isa Birnin Madina da Sanyin Safiyar Yau Alhamis Cikin Koshin lafiya.

Hakazalika maniyyatan sun karbi manyan jakankunan su tun a filin jirgin sama na Jeddah.

Yanzun Haka Wasu Daga Cikin Maniyyatan Sun Fara ziyarce ziyarcen su kafin Su Baro Madina Nan Bada Dadawa ba.