Hajjin bana: Rukunin farko na maniyyatan Katsina sun ɗauki hanyar zuwa Makkah Makkah bayan kwanaki 4 a Madinah

0
140

Maniyatan Jihar Katsina, jirgi na farko a yau Litinin sun baro birnin Madina zuwa Makkah bayan kammala kwanaki huɗu da aka ƙayyade wa maniyyata su yi a Madina.

Tuni maniyatan su ka ɗauki hanyar zuwa Makkah bayan sun dauki niyyar yin Ummara a Miƙati.

A sanarwar da kakakin hukumar ya fitar, wasu maniyyatan da aka tattauna da su sun yi godiya ga gwamnatin Jihar, ƙarkashin jagorancin Mallam Dikko Umar Radda akan kulawa tare da yaba wa kwamitin Hukumar Jin dadin Alhazai ta jihar Katsina, akan dawainiya da suke ta yi tun lokacin da su ka iso kasa mai tsarki.