Malamai ga alhazan Katsina: Ku cika wa gwamna Radda alƙawarin da ku ka ɗaukar masa

0
131

Mallaman da Gwamnatin Jihar Katsina ta ɗauka domin fadakar da maniyyatan jihar sun yi kira gare su da su cika alkawarin da suka ɗaukar wa gwamna Umar Dikko Radda

A lokacin da su ke yi wa maniyyatan wa’azi, Malaman sun yi kira gare su da su ɗauki alƙawarin da suka ɗaukar wa gwamnan na yi masa addu’ar Allah Ya ƙara saka mishi tausayin talaka da bashi ikon taimaka wa talakawa.

Sannan sunyi kira ga maniyyatan da su sanya jihar Katsina da ƙananan hukumomin ta da iftila’i na ƴan bindiga ke addaba da ma kasa baki ɗaya.

Sannan malaman sun yi dogon jawabi kan yadda maniyatan za su gudanar da aikin Hajji tun daga niyya har zuwa ranar Arafat da bayan ta.

“A kwamitin Mishair na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar katsina sun kusan kammala Shirin Karbar bakin Allah daga Jihar a minna da Arafat.

“A Wani Labarin Kuma Gwamnatin Jihar Katsina Tare Da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar katsina sun kusan kammala Dukkan Shiri Na fara Jigilar Alhazai Daga Makkah Zuwa Minna.

“Kamar Yanda Aka Tsara a Yau Alhamis Tun Daga Karfe Goma Sha Niyu Na Dare Za’a Fara Daukar Alhazan Daga Makkah Zuwa Minna.

“A Wannan Aikin Hajjin Na 2024 Hukumar Kula Da Aikin Hajji ta Kasar Saudiyya ta Kara Tsaurara Mataman Tsaro Domin Dakile Wadan Da Ke Shigowa Babu Izinin Yin Aikin Hajji.

“Yanzun Haka Babu Manyan motoci tare da dukkan Mota Wadda Bata Da Sticker ta Bada izinin shiga Minna da Arafat.

“Haka Kuma Maniyyaci kafin ya shiga mota daga Masauki dole sai an duba wani babban kati da akayi ma Kowane Maniyyaci Domin bashi damar shiga farfajiyar.

“Haka Kuma ko an tantance Maniyyaci yo idan ya shiga mota Bata Tashi Sai An Rufe Kofar Da Sticker Sannan Zata Mota,”