Hajjin bana: Gwamnatin Kebbi ta biya wa alhazan jihar kuɗin hadaya

0
191

Gwamanan Jihar Kebbi, Dr Nasir Idris ya bayyana cewa gwamnatin Jihar ta biya wa dukkan alhazan ta kudin hadaya, wato dabbar da alhazai ke yanka wa a matsayin wani rukuni na aikin Hajji.

Gwamnan ya baiyana haka ne yayin zanta wa da manema labarai a filin Arfa a yau Asabar.

A sanarwar da kwamitin yada labarai ma Hajjin bana na jihar ya fitar, gwamanan ya bayyana cewa gwamnatin sa tayi iya kokarin ta ganin ta samar wa alhazan jihar jin dadi da sauki a lokacin aikin su na Ibada.

“Maigirma gwamana ya bayyana cewa tun farko gwamnatin sa ta biyama dukkan Alhazan Jihar Kebbi cikon kudi Naira Miliyan daya daya, da sauran hidimomi,” in ji sanarwar.